6 Mayu 2020 - 08:17
Kasar Lebanon Ta Gode Wa Iran Saboda Tallafa Ma Ta Kayan Fada Da Cutar Corona

Ministocin harkokin wajen kasar Lebano da na kiwon lafiya ne su ka bayyana godiyarsu ga Iran saboda taimako da kayan fada da cutar covid-19 da ta bai wa kasarsu.

Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Ministocin harkokin wajen kasar Lebano da na kiwon lafiya ne su ka bayyana godiyarsu ga Iran saboda taimako da kayan fada da cutar covid-19 da ta bai wa kasarsu.

Tashar Talabijin din ‘al-manar ta kasar Lebanon ta ambato ministan kiwon lafiya na kasar, Hamad Hassan yana yin jinjina ga Iran wacce ta bai wa kasar na’urorin taimakawa lumfashi; ( Ventilators) 15, da kuma kayayyakin da ake amfani da su na gwaji domin gano masu dauke da cutar ta Covid-19.

Minisan ya ce “Mun kai gwauro da mari a kasashen turai da wasu kungiyoyin kasa da kasa domin ganin mun samu irin wadannan kayan, amma sai bayan gushewar lokaci mai tsawo mu ka sami ‘yan kadan.”

Hamad Hassan ya kara da cewa; Duk da cewa Iran tana fada da cutar ta corona, amma tana taimakawa wasu kasashen, da hakan yake nuni da halayyar kwarai.”

A nashi gefen, jakadan Iran a birnin Beirut, Muhammad Jalal Firouznia, ya ce taimakon na ‘yan adamtaka yana a karkashin shirin kyakkyawar alakar kawance da take tsakanin kasashen biyu ne.

Daga cikin kayan da Iran din ta aike zuwa Lebanon da akwai na’urar taimakawa lumfashi, safunan hannu,takunkuman rufe fuska, sai kuma na’urorin gwaji domin gano masu dauke da cutar ta covid-19.


/129